An sami karin mutane 930 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya, jimilla 74,062.
Majalisar dattawa ta dage amincewa da kasafin kudin 2021 har sai ranar Litini mai zuwa.
Gwamna Bala Muhammad na jihar Bauchi ya ce yana fuskantar matsin lamba na cewa sai ya binciki gwamnonin baya a jihar.
Gwamnan jihar Katsina, Bello Masari, ya musanta maganar Shekau ta alhakin satar daliban GSSS Kankara.
Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Sani Yarima, ya bayyana kudirinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.
Kotun daukaka kara ta rushe hukuncin da babbar kotun tarayya ta yankewa Olisa Metuh.
An ƙona ofisoshin ‘yan sanda uku a Anambra kan kisan mai babur da ‘yan sanda suka yi.
Boko Haram ta bi ‘yan Najeriya 50 da ke gudun hijra a Jamhoriyar Nijar ta kashe su.
Kotu a Faransa ta samu mutum 14 da laifin kai hare-hare kan mujallar Charlie Hebdo a 2015.
Juventus ta soma tattaunawa da wakilin Paul Pogba, a yayin da take yunkurin sake daukar dan wasan na Manchester United.
EPL: Southampton da Arsenal sun tashi 1:1 a wasan jiya.
EPL: Liverpool ta sami nasara a kan Tottenham da ci 2:1 a wasan jiya.
LaLiga: Barcelona ta sami nasara a kan Real Sociedad da ci 2:1 a wasan jiya.