Jagorancin kungiyoyin lafiya jari, Kano proper da CRC karkashin Jagorancin tsohon kwamishinan kasuwanci da yada labarai kuma tsohon wakili a majalisar wakilai ta Kasa Dr Danburan Abubakar Nuhu sun kai ziyarar Taaziyya ga tsohon gwamna Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso bisa rasuwar mahaifinsa Madakin Bichi Alhaji Musa Sale Kwankwaso,
Da yake jawabi yayin ziyarar Dr Danburan yace ga mayyar kungiyoyin da suka amfana da mulkin injiniya Rabiu Musa Kwankwaso sun kadu matuka da jin rasuwar Uba kuma Kaka garesu, hakkan ne ya sanyasu gama kai Dan suzo suyi taaziyyar babban rashin Daya shafi alummar jihar kano,
Kungiyoyin da suka ce bazasu manta da yadda injiya Kwankwaso ya tarbiyantar dasu ba wajen kishin zuci da tabbatar da dogaro da kai da kishin jihar kano ba su jadda cigaba da goyon bayan tsarin da tsohon gwamna kuma tsohon sanata Rabiu Kwankwaso ya ke son Dora alummar kano,
Kimanin kungiyoyin 40,000 ne keda rijista da maaikatar kasuwanci da masanaantu a lokacin mulkin Injiya Rabiu Musa Kwankwaso karkashin kwamishinan kasuwanci Dr Danburan Abubakar Nuhu a wancan lokaci inda kowace kungiya ke amfana kai tsaye Daga gwamnati dan bunkasa sanaoinsu,
Ziyarar taaziyyar na cigaba inda a baya bayannan tawagar Gidan Radio Express Karkashin Jagorancin Alhaji Ali Baba Kusa takai makamanciyar ziyarar taaziyyar ga tshohon gwamnan inda manajan daraktan yayi adduar samu rahama ga marigayi Hakimin Madobi,