
Yana da kyau kungiyoyi da madawata su wai wayi marayu da sauran marassa karfi sabo da yanayin da ake cikin na zaman gida.
Shugabar Gidauniyar Mutunci Foundation Hajiya Nana Yarima, ta ambata hakan tabakin Ummi Umar Kiru, a lokacin da take zantawa da tashar radiyo Express a ofishin kungiyar a birnin Kano.
Tace “la’akari da yadda aka sanya dokar hana zurga zurga akwai bukatar taimakawa Mutanen da sai sun fita suke samu domin rage musu radadin rayuwa.
Ummi Umar Kiru, ta sake “jan hankalin al”umma dasu bi doka da aka sanya ta zaman gida da hana zurga zurga domin ta hanane za’a Iya dakike yaduwar cutar covid-19 a jihar Kano.
Ta kuma bayar da tabbacin cewa Kungiyar Mutunci Foundation ” zata cigaba da tallafa al’umma musamman a wannan lokaci da ake ciki na zaman gida.