Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

A wata hira ta musamman da shugabannin kungiyar kantin kwari da akayi a radiyon express a ranar asabar, shugabannin kungiyar yan kasuwar kantin kwari ta bakin kakakin kungiyar Aminu Sofa da sakataren kungiyar sunce ana Neman yi musu rufa rufa kan wasu dokoki da kaidojin da baza suyiwa kasuwar da yan kasuwar amfani ba,

Shugabannin sun zargi wani kusa mai rike da mukamin kwamishina a gwamnatin jihar da Neman kakabawa kasuwar wani sabon nauin haraji bayan na kaida da suke biya tare dayin babakere da handama da sunan gwamnati a kokarinsa na shafawa gwamnatin kashin kaji,

Aminu Sofa ya cigaba da cewa duk da dai shiba lauya bane ko me sharaa amma akwai lam a a dokokin da ake Neman majalisar dokokin jihar kano ta sanyawa hannu,

Dayake amsa tambaya kan ko gwamnati na nufi sake fasalin tsarin da zai kyautata kasuwarne ? Aminu sofa cewa yayi Sam gwamnatin kano karkashin Dr Abdullahi Umar Ganduje bata san wannan abin da kwamishinan ke kokari cusowaba inda yace ai shi gwamna Ganduje yasan yadda alakarsa take da yan kasuwar kwari kuma ya San yadda yan kasuwar ke martabashi,

Aminu sofa yace kwamishina ne da yankorensa ke Neman rufo kura da fatar akuya dan biyan bukatarsa da bata sunan gwamnati,inda yace a fahimtarsa kamata yayi a nemi yan kasuwar dan zama dasu a duk wani tsari da akeson bijiro dashi dan samun shawara daga yan kasuwar tunda ance mai daki shiyasan inda yake masa yo yo

Sofa ya godewa shugabancin majalisar dokoki ta jihar kano bisa yadda suka saurari kukan yan kungiyar.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *