Ofishin dake kula da alamuran shari’a na Kungiyar hadin kan afrika ta AU, ya ayyana nadin da akaiwa Dr. Ngozi Okonjo- Iweala na Babbar Daraktar Kungiyar kasuwanci ta Duniya a matsayin wanda aka yi ba bisa ka’ida ba.
Najeriya dai ta mika sunan Okonjo a ranar 4 ga watan Yuni ga hukumar tare da cewa tam aye gurbin dan takararta Ambasada Yunov Frederick Agah, wanda aka maye sunansa da Dr. Okonjo Iweala.
Iweala ta kasance tsohuwar Ministar Tattalin arzikin Najeriya ce kafin nadinta , a sabbin kasahen da suke neman kujerar, kasar Masar ta nemi sashin sharai’a na kungiyar daya bayyana matakin da Najeriya ta dauka ko yana bisa ka;ida ko kuwa aa.
Amsar da sashin shari’a na kungiyar AU, ya bayar a ranar 15 ga watan Yuni, yace matakin sauya dan takarata a neman kujerar ya saba da sashin doka na 11 da 12 na kungiyar.