Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Yayin da kungiyoyin dake buga wasan kwallon kafa ajin matasa a fadin tarayyar kasar nan suka dukufa dan fara gasar wasan kwallon kafa rukuni na daya na ajin matasa a shiyyoyi daban daban da aka ware dan gasar kungiyoyi 9 ne zasu kara a jos babban birnin jihar plateau,

Kungiyoyi irin su Goidano fc ba baki bane a gasar duba da yadda suka taka rawa a cikinta tare da samun nasarar da ta kaita ga shiga gasar kwararru ta kasa a shekata 2018 inda ta shafe tsawon shekaru biyu a gasar,

A tattaunawarsa da expressradiofm.com gabanin tashin tawagar kungiyar zuwa jihar plateau shugaban kungiyar Jamilu Wada Aliyu yace kungiyarsa ba bakuwa bace a gasar ajin matasa kuma bata da tsoro ko shakka a cikin gasar ta bana duk da cewa skwai sabbi da wasu kungiyoyi kamarsu a gasar amma kungiyarsa ta Giodano tayi shirin da zata bada mamaki kamar yadda tayi a shkaru 4 da suka gabata ” Bama jin tsoro ko shakka muna da managartan yan wasa kuma ashirye suke da gasar we are ready ” inji Jamilu Wada,

Da yake amsa tanbaya kan kalu balen da kungiyarsa zata fuskanta daga sauran kungiyoyi irin su Aklesondi da suka taba fafatawa a baya Jamilu Wada cewa yayi ” yes munsan juna mudasu amma suma sun san wacece Giodano kuma sunsan abin da Giodano zata iyayi”

Kungiyar Giodano na daya daga cikin kungiyoyi 2 daga Kano daga cikin 9 dake shiyyar Jos

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *