Hadakar wasu kungiyoyin arewa sun ce zasu yi tattaki zuwa garin Daura, mahaifar shugaban kasa, Muhamadu Buhari, domin gudanar da zanga-zanga a kan sace dalibai akalla 333 a sakandiren kimiyya da ke Kankara, jihar Katsina.
Har yanzu fiye da dalibai 300 ne ake zargin cewa su na hannun ‘yan bindigar da suka shiga cikin dakunansu na kwana, a makarantar sakandiren kimiyyya da ke Kankara, su ka yi awon gaba da su, kamar yadda TheCable ta rawaito.
Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun dira makarantar sakandiren kimiyya da ke Kankara, jihar Katsina, da talatainin daren Juma’a zuwa duku-dukun safiyar Asabar, tare da yin awon gaba da dalibai kusan 600.
Kakakin gamayyar kungiyoyin, CNG (Bringbackourboys campaign), Abdul-Azeez Suleiman, ya shaidawa Punch cewa zasu yi tattaki tare da yin gangami a Daura daga ranar Litinin har zuwa lokacin da za’a dawo da daliban da aka sace.