Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Al’ummomin wasu unguwanni uku a birnin Maroua na Jamhuriyyar Kamaru, sun shiga tsaka mai wuya, sakamakon mamayar unguwanninsu da ƙudajen zuma suka yi.

Harbin jama’a da suke yi da dafinsu ya kai ga a yanzu haka mutum biyar ne suke kwance a asibiti, huɗu daga cikinsu ƙananan yara ne.

Wannan lamari ya kai ga jami’an tsaro yin kira ga al’umomin mazauna unguwannin da su koma zaman gida zuwa lokacin da za a ga lafawar wannan bala’i.

Yanzu haka dai sojojin kashe gobara sun fito ba don kashe gobara ba a birnin Marouam, sai don su yiwa ƙudan zuma taron dangi wadanda suka yiwa wasu unguwanni a Maroua ƙawanya.

Ba dai a san daga inda tarin ƙudan zuman suka fito ba, abin da al’ummar unguwanni ke ta mamakin yawansu.

Tun da farko al’ummar unguwannin da ƙudan zuman suka mamaye sai da suka yi amfani da dabaru irin na gargajiya wajen korar ƙudan zuman inda suka rinka kona tsummokaran tufafi.

Mutanen sun yi wannan dabara ce domin zafin wuta da hayaƙi su turnuƙe ƙudajen zuman daga nan kuma sai su samu su fice.

To sai kuma duk da wannan dabara ta mutanen ba su samu nasara ba domin ƙudajen zuman ba su matsa ko nan da can ba.

Wannan dalili ne ya sa aka nemi ɗaukin sojojin kashe gobara waɗanda ke ƙarawa da wuta komai zafinta da kuma yawanta don a samu a fatattaki ƙudajen zuman.

Tuni aka hana mutanen unguwannin da ƙudajen zuman suka mamaye fita saboda gudun kada su huce a kansu. ppm

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *