Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya umurni makiyaya Fulani da ke jiharsa su zakulo bata garin da ke jiharsu domin idan suna son zaman lafiya, inda ya kuma gargadi kan cewa a dena jefa siyasa cikin rikicin makiyaya da manoma.
Ya bayyana hakan ne yayin ziyarar gani da ido na tsaro da ya kai a karamar hukumar Ovia ta Kudu a jihar, Daily Trust ta ruwaito
Gwamnan, wanda ya danganta tattakin da makiyaya ke yi zuwa wurare daban-daban da dumaman yanayi ya yi kira ga yan Nigeria su binciko hanyoyin da za su sulhuta makiyaya da manoman a maimakon siyasantar da rikcin.