
Kotun Kolin Najeriya ta tabbatar da matakin da marigayi Sarkin Kano da ke Najeriya, Alhaji Ado Bayero ya dauka na tube rawanin Aminu Babban Ɗan’agundi daga mukaminsa na Sarkin Dawaki Maituta kuma hakimin Gabasawa.
Da take tabbbatar da hukuncin, Mai shari`a Mary Odili, wacce ta jagoranci alkalan Kotun Kolin su biyar, ta ce matakin da marigayi Ado Bayero ya dauka yana kan ka’ida.
A shekara ta 2003 ne marigayi mai martaba Sarkin Kano Ado Bayero ya sauke Aminu Babba Dan`agundi daga mukamin nasa, bayan an zarge shi da nuna rashin da`a ga sarki, da aikata wasu laifuka da suka saba da dabi`un mai rike da mukami irin nasa.
Cikin dabi’un har da korafin da aka ce al`umar masarautarsa ta rubuta a kansa, tana zarginsa da shiga harkar siyasa da shirya magudi, a zaben da aka yi a shekera ta 2003. Amma ya musanta.
Daga nan ne Aminu Babba Dan`agundi ya kai kara wata babbar kotu a Kano, inda ya kalubalanci Sarki da fadar Kano dangane da tube masa rawani da aka yi masa, musamman ma huruminta na yin hakan, inda alkalin kotun mai shara`a Muhammad Sadi Mato ya ba shi gaskiya, kana ya umurci fadar Kano ta mayar da shi kan mukaminsa, tare da biyansa dukkan hakokinsa.