Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Kotun Ƙolin Amurka ta yi watsi da wata ƙara irin ta ta farko a tarihi da Shugaban ƙasar Donald Trump ke mara wa baya, wadda aka buƙaci Kotun Ƙolin ta sauya sakamakon zabukan da aka yi a jihohi huɗu da Trump ya faɗi zaben shugaban ƙasa.

An dai shigar da ƙarar ne a jihar Texas, kuma jihohin da wadanda suka shigar da ƙarar suka nemi a soke sakamakon zabukan su ne Georgia da Michigan da Pennsylvania da kuma Wisconsin.

Zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Joe Biden ne ya lashe zaɓukan da aka yi a duka jihohin huɗu.

Bbc ta ruwaito Ƴan majalisar Amurka daga jam’iyya mai mulki ta Republican su 127 tare da lauyoyin gwamnatocin jihohi 19 sun goyi bayan wannan ƙarar.

Amma Kotun Ƙolin ta yanke hukunci tana cewa jihar ta Texas ba ta da hurumi a shari’ance na shigar da irin wannan ƙarar, kuma ta yi watsi da ƙarar nan take.

“Jihar Texas ta kasa nuna wa a shari’ance yadda wannan zaben ya shafe ta ganin cewa kowace jiha tana da ikon gudanar da zaɓuka a ƙarƙashin dokokinta,” inji Kotun Ƙolin.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *