Bayan watanni hudu da daukaka karar da Yahaya Sharrif yayi, kotun tayi watsi da hukuncin kotun Shari’a
Hakazalika kotun ta wanke wani yaron da aka yankewa hukuncin shekara 10 a Kurkuku
Alkali Nuradden Sagir, shine wanda ya yanke hukuncin ranar Alhamis
Kotun daukaka kara dake zamanta a jihar Kano ta yi watsi da hukuncin daurin shekaru 10 da akayi wa Umar Farouq, matashin da ake zargi da kalaman batanci ga Annabi.
Bayan haka, kotun ta sake watsi da hukuncin da aka yiwa mawaki, Yahaya Aminu Sharif, inda ta ce a sake shari’ar daga farko, cewar rahoton BBC.
Shi ma Yahaya Aminu Sharrif ana zarginsa da kalaman batanci kan Annabi (SAW).
Alkali Nuradden Sagir, shine wanda ya yanke hukuncin ranar Alhamis.
Ya ce hukuncin da aka yanke a farko na cike da kura-kurai kuma ko lauya ba’a bashi ba.
A cewarsa, hukuncin da kotun Shari’ar tayi ya sabawa Sashe 2-6-9 na ACJ.