
Wata mata dataci zarafin Jami’an tsaro da kotu zata gudanar da aikin alumma a matsayin hukunci a gidan kurkuku a Jihar Kano.
Kotun tafi da gidanka dake hukunta wadanda suka karya dokar zaman gida a Jihar Kano ta yankewa wata mata hukunci sakamakon cin zarafin Jami’an tsaro da kotu da tayi lokacin da suke gudanar da aikin su.
Matar mai suna Amena kotun ta zartar mata da hukuncin aikin al’umma a gidan kurkuku har tsahon mako daya da biyan tara.
Sannan Alkalin kotun ya umarceta data baiwa Jami’an tsaron hakuri.
Sai dai Ameena tayi da’awar cewa tana da Yaro wanda take shawarwa amma kotun tace azo da yaron agwada idan ya karbi mama yasha tabbas haka ne, kuma za’a sassauta mata hukuncin, zuwa wasu ‘yan sa’o’i a kullum.