Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Shugaban Cote d'Ivoire, Alassane Ouattara na zantawa da  RFI, 3, disamba 2019.

Kotu a birnin Abidjan na kasar Cote d’Ivoire ta daure mutane 29 watanni uku-uku a gidan yari, sannan kowane zai biya tarar jaka 100 na cfa kimanin euro 150 kenan, bayan samun su da laifin lalata wata cibiyar da mahukunta suka kafa don jinyar masu dauke da cutar coronavirus.

Kotun ta samu mutanen 29 da laifin rusa wannan cibiya da aka kafa a unguwar Yopougon da ke birnin Abidjan kimanin makonni biyu da suka gabata tare da korar jami’an kiwon lafiya da ke aiki a cibiyar.

To sai dai mazauna unguwar ta Yopougon sun yi zargin cewa tun lokacin da aka bude wannan cibiya ba su ga ko da mutum daya da aka kwantar a wannan cibiya saboda ya harbu da wannan cuta, yayin da wasu daga cikinsu ke cewa an bude cibiyar ne domin yada cutar da gangan.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *