daga :Abdullahi Isah da Abbas Musa Sheka

Bayan shafe kimanin shekara guda a Gidan Maza, Matashin Dan Siyasar nan Mustapha Muhammad Bature da akafi sani da Mustapha Jarfa ya samu beli a Wata Kotu dake nan Kano.
Mai Shari’a Huda Haruna Abdu, ta Kotun Majistire dake unguwar Gyadi Gyadi, ta bayarda belin Mustapha Jarfa bayanda Lauyansa Barista Bashir Muhammad ya gabatar mata bukatar neman belin.
Sai dai sharudan belin sun tanadi cewa dolene ma’aikacin Gwamnati Mai mataki na 14 ya tsaya masa tareda Karin wani mutum dake da shaidar biyan kudin haraji na shekara 5, sannan wajibi ne Musyapha Jarfa ya guji magana a kafafan yada labarai har zuwa lokacin da za’a kammala Shari’ar.
Idan ana iya tunawa, an Kama tareda tsare Mustapha Jarfa ne tun gabanin zaben 2019 bisa zarginsa da laifin cin mutuncin mataimakin Gwamnan Kano Dr Nasiru Yusuf Gawuna.
Sai dai yayinda aka kammala wancan Shari’ar, ita kuwa rundunar yan sandan jihar Kano ta sake gabatar da sabbin tuhume tuhume da take yiwa Matashin Dan siyasar.