An naɗa Ronald Koeman a matsayin sabon kocin Barcelona kwana biyu bayan korar Quique Setien.
Ɗan shekara 57 din ya ajiye aikin horar da tawagar ƙasar Netherlands da saura shekara biyu a kwangilarsa domin ya sanya hannu a kwangilar shekara biyu da Barcelona.
Ya buga wa Barcelona tamaula a tsakanin shekarun 1989 zuwa 1995 har ma ya taimaka musu lashe kofin La Liga huɗu da kofin Zakarun Turai na Champions League ɗaya.
Barcelona ta kammala kakar wasa ta bana a mataki na biyu a La liga, inda ta kasa cin kofi ko ɗaya a karon farko tun kakar 2007-2008.
Ratar maki biyar da Real Madrid ta ba ta da ƙwallo takwas da kuma ragargazar da Bayern Munich ta yi mata a Champions League makon da ya wuce ne suka sa aka kori Setiein ranar Litinin.
Kungiyar ta naɗa Ramon Planes a matsayin daraktan tsare-tsare. Shi ne mataimakin Eric Abidal, da ya sauka daga kujerar daraktan wasanni ranar Talata.
Koeman zai yi jawabi a taron manema labarai da karfe 5:00 agogon Najeriya da Nijar.