Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Koriya Ta Arewa ta dakatar da shirinta na ɗaukar matakin soji kan Kudu, kamar yadda kafar yada labaran kasar ta ruwaito.

A makonnin da suka gabata an yi ta ganin irin abubuwan da Koriya Ta Arewa ta yi cikin ɓacin rai kan yadda kungiyoyin da suka gudu daga Koriya Ta Arewa zuwa ta Kudu da suke tura sakwannin farfaganda suka ringa izawa.

Bbc taruwaito a makon jiya ne Koriya Ta Arewa ta tarwatsa wani ofishin hadaka tsakaninta da Koriya Ta Kudu, a garin Kaesong da ke kusa da iyakar kasashen biyu.

A wani taro da Kim Jong-un ya jagoranta ya ce an dauki matakin ne don dakatar da tura sojojin.

Kwamitin Soji na kasar ya yanke shawararsa bayan yin nazari kan yanayin da ake ciki.

Arewar ta kuma cire lasifikun da ta daddasa a makon da ya gabata, wadanda ake amfani da su wajen aike sako ga Kudu a kan iyaka, kamar yadda Yonhap ta ruwaito.

“Taron ya kuma tattauna kan takardun yadda matakan za su kasance don ci gaba da dakatar da batun yakin,” in ji kamfanin dillancin labarai na KCNA.

Koriya Ta Arewa ta tarwatsa ofishin tuntuba tsakaninta da ta Kudu
Koriya Ta Arewa za ta tura dakaru kan iyakarta da Kudu
Wasu masu sharhi sun fito da batun yiyuwar Mr Kim na iya biye wa kanwarsa ne kan wasu tsare-tsaren. Kar ku manta cewa dakatar da aike sojoji aka yi ba fasawa ba gaba daya – don haka da sauran rina a kaba.

Irin wannan rikicin na yawan bai wa ‘yar uwar Kim Jong-un dama don nuna kwazonta na cewa za ta iya shugabanci, amma dai har yanzu mun san wanda ke jan ragamar mulkin.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *