Kocin Barcelona Ronald Koeman yana son dauko dan wasan Lyon da Netherlands Memphis Depay, mai shekara 26, a watan Janairu. (AD, via Goal)
Kazalika Barcelona tana zawarcin dan wasan Liverpool da Netherlands Georginio Wijnaldum. Dan kwallon mai shekara 29 yana shekarar karshe ta kwangilar da ya sanya wa hannu a Anfield don haka zai kasance ba shi da kungiya a bazara. (AD, via Sky Sports)
Manchester United na sha’awar dauko dan wasan Real Madrid da Uruguay Federico Valverde, mai shekara 22, kuma za ta iya yin musayarsa da dan wasan Faransa Paul Pogba, mai shekara 27. (Sun)
Ronald Koeman ya nemi majalisar zartarwar Barcelona ta kammala dauko dan wasan Manchester City da Sufaniya Eric Garcia, mai shekara 19, a watan Janairu. (Mirror)
Kocin West Ham David Moyes ya ce ya ajiye helikwafta da niyyar dauko Gareth Bale don hana shi tafiya Real Madrid daga Tottenham a 2013 lokacin yana manajan Manchester United. Kwanakin baya dan kwallon na Wales, mai shekara 31, ya koma Tottenham domin yin zaman aro. (Mail)
Dan wasan Manchester United da Ingila Marcus Rashford, mai shekara 22, ya ce wa’adin da aka sanya na isar dan wasan Uruguay Edinson Cavani, mai shekara 33, kungiyar zai taimaka musu lashe kofuna. (Sky Sports)
Juventus ya gwammace dauko dan wasan Italiya Federico Chiesa, mai shekara 22, daga Fiorentina, maimakon dan wasan Lyon da Faransa Houssem Aouar, mai shekara 22, lokacin musayar ‘yan kwallo a bazara. (Sky Sport Italia, via Mail)
Kocin Middlesbrough Neil Warnock ya ce ya kamata a dora wani bangare na laifi kan Yannick Bolasie, mai shekara 31, kan rashin nasararsa ta barin kungiyar. Dan wasan ya so tafiya Boro daga Everton ranar da ake rufe kasuwar ‘yan kwallo. (Teesside Gazette)