Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Fada tsakanin kungiyoyin yan bindiga biyu ya yi sanadiyar mutuwar gagarumin dan bindiga Nasiru Kachalla a Jihar Kaduna

An kashe Nasiru Kachalla, Mashahurin dan bindiga, wanda ake zargin shine kashin bayan ayyukan ta’addanci da a Jihar Kaduna, inji gwamnatin Jihar Kaduna.

A wata sanarwa da Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida ya fitar ranar Litinin ya ce an kashe Kachalla a wata fafatawa tsakanin tawagar sa da kuma wata tawagar yan ta’addan.

Shi ne ke jagorantar ayyukan ta’addanci da dama ciki harda garkuwa da mutane, kashe kashe, satar shanu da sauran wasu da dama

A cewar Aruwan, masu binciken kwakwaf sun tabbatar da cewa an kashe yan ta’addan daya bangaren, da kuma wasu daga cikin sojojin Kachalla.

“Karawar ta afku a wani daji da ke kan iyakar kananan hukumomin Kajuru-Chikun na jihar Kaduna,” ya bayyana a cikin sanarwar.

Aruwan ya yi bayanin cewa fadan ya barke akan wani garken shanu da aka sato.

Ya ce Kachalla da tawagar sa suna da hannu wajen ayyukan bata gari, ciki har da garkuwa da mutane, kashe kashe da kuma ta’addancin da ke faruwa kan titin Kaduna zuwa Abuja dama na Chikun/Kajuru.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *