Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Kasar New Zealand ta sanar da cewa ta dakile yaduwar cutar korona tsakanin al’ummar kasar wanda ya kawo karshen cutar gaba daya.
A yanzu dai ba a samun masu kamuwa da cutar da suka wuce 9 a cikin kwanaki masu dama – inda daya kawai aka samu ranar Lahadi – matakin da ya sa Firai minista Jacinda Ardern ta ayyana cewa “a halin yanzu” sun kawar da cutar.
Amma jami’ai na kashedi ga ‘yan kasar da ka da su yi sakaci, domin sun ce wannan nasarar ba ta na nufin babu wanda zai sake kamuwa da cutar ba ke nan.
Wannan labarin na zuwa ne sa’o’i kadan bayan da gwamnati ta sassauta dokokin hana walwala mafi tsauri da kasar ta taba gindaya wa.
Daga Talata, wasu kamfanoni za su fara aiki, inda dukkan bangarorin kiwon lafiya da na ilimi za su koma bakin aiki.
Amma za a ci gaba da bukatar yawancin ‘yna kasar da su ci gaba da zama a gida a koda yaushe.
“Mun fara bude sassa masu muhimmanci na farfado da tattalin arzikinmu, amma ba mu shirya kyale mutane su yi walwala ba tukuna”, inji Ms Ardern yain ganawa da manema labarai da ta ke yi a kowace rana.
New Zealand na da kasa da mutum 1,500 da ke dauke da cutar korona inda cikinsu mutum 19 ne suka mutu.
Ms Ardern ta kuma ce “babu mutane masu yawa dauke da cutar a New Zealand”, inda ta ce: “Mun yi nasara a wannan yakin”.
Amma ta ce dole kasar ta ci gaba da daukan matakan kariya domin “muna son komai ya ci gaba da inganta”.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *