
Wasu bincike biyu sun gano cewa karuwar gurbatar iska ka iya kara ta’azzara mace-macen da ake samu dalilin cutar corona.
Dakta Maria Neira da ke aiki da Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta shaida wa BBC cewa, ya kamata kasashen da ke fuskantar gurbatar iska a nahiyoyin Latin Amurka da Afrika da Asiya su kara shiri kan cutar.
Mutanen da ke fama da cutuka masu alaka da nunfashi a kasashen da ke da yawan gurbatar iska, sun fi wahala daga cutar coronan.
Sai dai masana a bangaren lafiya sun ce ya yi wuri a alakanta matsalar da masu fama da lalurar numfashi.
“Za mu samar da taswirar biranen da suka fi fama da matsalar gurbatar iska, wadda muka samu ta bayanan da muka tattarara, da za su iya taimaka wa hukumomin kasashen da ke wadannan yankuna, domin su shirya wa wannan annoba kamar yadda ya kamata,” In ji Dakta Neira.
Wani binciken da aka gudanar a Amurka ya ce an samu karuwar mutuwa da kashi 15 cikin 100 sakamakon cutar korona, a yankunan da ake samun karuwar kanana kwayoyin zarra da ke gurbata iska a shekarun baya tun kan a samu bullar wannan annoba.
Wadannan kananan kwayoyin zarra, da fadinsu ya yi kwatankwacin mita daya cikin 30 na fadin gashin dan adam, an gano cewa a baya suna haifar da cutukan numfashi da ciown kansa.
Ya zuwa yanzu binciken jami’ar Havard bai bibiyi rahotonnin da aka gabatar ba, amma Farfesa Annette Peters da ke jami’ar Ludwig Maximilian ta birnin Munich da ke bibiyar harkokin annoba, ta shaida wa BBC cewa sabbin bincike da su ka yi sun dace rahotannin da aka fitar a baya kan yadda ake kwantar da mutane a asibiti da kuma mutuwar da ake samu ta nimoniya.
“Wannan daya ne daga cikin binciken farko da ke bayani kan abin da muke zargi, da kuma hasashen cewa akwai yiwuwar kwayoyin zarrar da ke gurbata isaka na janyo hadarin kamuwa da annobar,” a cewarta.
Rahoton marubuciya Farfesa Francesca Dominic ya ce: “Muna fatan hukumomi za su tsaurara dokoki da za su taimaka wajen dakile ta’azzarar gurbatar iska lokacin da ake tsaka da wannan annoba.”
Wani karin bincike da aka gudanar a jami’ar Siena da ke Italiya da kuma jami’ar Arhus ta Denmark, sun ce akwai alaka tsakanin karuwar gurbatacciyar iska da kuma karin mutuwar da ake samu dalilin cutar korona a arewacin Italiya.
An samu karin mutuwa da kashi 12 cikin 100 a yankunann Lombardy da Emilia Romagna idan aka kwatanta da sauran sassan Italiya da mutuwar ke kashi 4.5 cikin dari.
Binciken da aka wallafa a mujallar intanet ta Sciense Direct ta ce: ” Ya kamata a duba yawan gurbatar iskar a arewacin Italiya a matsayin wani abu da ya kara ta’azzara mace-mace a yankin.”
Adadin yawan jama’a da shekaru da lalacewar tsarin kiwon lafiya da kuma nau’o’in matakan kariya dake yankin suma abubuwan lura ne a wannan yanayi.
Shin ibuprofen yana maganin
Haka kuma a Philippines, Cesar Bugaoisan da ke Kungiyar Likitocin bangaren Numfashi ya ce, “A bayanan da muka tattara, kusan duka mutuwar da aka samu ta daidaikun da ke da alaka da cutar korona suna da wata matsalar lafiya, kuma mafi yawa na da alaka da gurbatar iska.”
Matsalar gurbatar iska dai tana kashe mutum miliyan 20 duk shekara, in ji WHO.
Kuma sama da kashi 90 cikin 100 na mutanen duniya na rayuwa ne a wuraren da gurbatacciyar iska ta wuce ka’idojinta musamman a kashen da ke fama da talauci.
Akwai kasashe da wannan cuta ta shafa da yawa a kudancin Asiya da Gabas ta Tsakiya da kuma Arewacin Afrika, kamar yadda wani rahoton Bankin Duniya ya bayyana a bara.
Birane a Chile da Brazil da Mexico da kuma Peru su ma suna fuskantar matsalar gurbatar iska, kamar yadda rahotannin WHO da Majalisar Dinkin Duniya su ka bayyana.
Amma rahoton da aka fitar kan Ingancin Iskar Duniya na 2019, ya ce Indiya ce ke da mafi yawan birane da ke cikin hadarin matsalar gurbatacciyar iska.
An samu mutuwar mutum 521 dalilin cutar corona ya zuwa yanzu a Indiya.
Dakta S K Chhabra, shugaban sashen kula da huhu na asibitin kwararru na Primus Super da ke Delhi ya ce: ” Idan aka samu karuwar yaduwar cutar, babu shakka mutanen da ke fama da matsalar rashin lafiyar numfashi su ne za su fi shan wahala.”
Shugaban gidauniyar kula da lafiyar jama’a a Indiya Farfesa Srinath Reddy ya ce.”Idan matsalar gurbatar iska ta lalata hanyoyin shakar iska da huhu, za a shiga wani hali dangane da yadda za a shawo kan annobar cuta korona.”
Amma Dakta Rajni Kant Srivastava da ke cibiyar bincike ta Indiya yace, “Babu wata kwakkwarar shaida kuma ba mu gudanar da wani bincike mai kama da wannan ba.”
Annobar cutar Sars da aka yi fama da ita a 2002, wadda wasu kwayoyin na daban ke haddasa ta, ta shafi mutum sama da 8,000 a kasashen 26 haka kuma ta kashe kimanin mutum 800.
Kuma wani bincike da aka gudanar a 2003 a jami’ar California, ya ce mutanen da suka fito daga yankunan da ke da yawan gurbatacciyar iska sun ninka sau biyu na yiyuwar mutuwa saboda kwayoyin cuta.