Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Da alamun dan wasan chelsea Ngolo Kante zaiyi jinyar makwanni uku sakamakon raunin da ya ji a cinyarsa, a cewar kocin kungiyar Frank Lampard.

Dan wasan na Faransa wanda ya lashe Kofin Duniya ya yi raunin ne lokacin fafatawar da Manchester United ta doke su da ci 2-0 ranar Litinin.

Jinyar da zai yi babban koma-baya ne ga Chelsea, wacce za ta buga wasan lig shida da kuma cup games a mako ukun da ke tafe.

“Ya ji rauni a tsokarsa, irin wanda ya ji lokacin wasanmu,” in ji Lampard.

Kante zai yi jinya ne a lokacin da Chelsea ke tsaka mai wuya a kakar wasa ta bana.

Chelsea za su fafata da Bayern Munich a wasan ‘yan 16 na gasar Zakarun Turai ranar Talata mai zuwa sannan su sake karawa a Jamus ranar 10 ga watan Maris.

Chelsea, wacce ita ce ta hudu a saman teburin Firimiya amma bata ci wasa a karawarta a wasa hudu mafi muhimmanci ba, za ta gwabza da Tottenham a wasan hamayya da za su yi a London ranar Asabar.

Kazalika, za su karbi bakwancin Liverpool a zagaye na biyar na gasar cin Kofin FA ranar uku ga watan Maris, yayin da za su fuskanci Bournemouth da Everton a gasar Firimiya a ranar 29 ga watan Fabrairu da takwas ga watan Maris.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *