Kungiyar kwallon kafa yan kasa da shekaru 15 ta kingiyar kano pillars dake jihar kano a arewacin najeriya ta kai matakin daf da inda zata kai wasan Tofa firimiya sakamakon nasarar da kungiyar tayi da ci 2-1 a wasan da ta buga da kungiyar Tamburawa United a wasan farko na zagayen share fagen shiga gasar Tofa firimiya da aka buga a filin wasa na Mahaha dake kofar naisa
Tunda fari Tamburawa United ce ta fara jefa kwallon a raga Pillars minti 1 da fara wasa ta hannu Usani Jirgi kafin kingiyar ta yan kasa da shekaru 15 ta pillars din ta warware ta hannun Habu Pillo,kafin tafiya hutun rabin lokaci
Wasan da ya sauya salo bayan da wowa daga hutun rabin lokaci, kungiyoyin sun sauya fasalin wasa inda kowa ke kai hare hare ga dan uwansa amma kwallon taki shiga sai a minta na 76 ne Habu Pillo ya jefa kwallo ta 2 a ragar Tamburawa jimillar kwallo biyu da dan wasan ya jefa shi kadai a wasan daya baya kungiyar U – 15 din nasara,
Da hakane kungiyar zata jira wasa na gaba wanda zatayi a matakin daf da na kusa da karshe na share fagen shiga Tofa firimiya babbar gasa ta hukumar kwallon kafar jihar kano,
Mai horar da kungiyar Coach legion yace nasarar abar alfaharice kasancewar wasan shine na farko a wasan share fagen kuma da babbar kungiya irin tamburawa united data dade a gasar ” A gaskiya wasane da yayi zafi kwarai amma yarana sunyi kokari” inji coach legion
Shikuwa mai horas da kungiyar Tamburawa Sabi’u Naira kira yayi ga hukumar wasa ta jihar kano data dinga sanya idanu a duk lokacin da irin wadannan wasannin sukazo wannan matakin inda yace ” A kwai ayar tambaya a wasan kuma bamu gamsu da yadda alkalancin ya kasanceba amma ina kira ga hukumar kwallon kafa data dinga sanya idanu a irin wannan wasan” inji Coach Naira