Shugaban Matasan Jamiyyar APC na shiyar arewa maso yamma Komared Abubakar Sadiq Saad fakai yace tabbas harkokin wasanni na daya daga cikin abubuwan da zasu taka rawa bunkasa cigaban tattalin arxiki da hada kan matasan arewa dan samun nasarar da ake bukata.
A tattaunawarsa da wakilinmu Salisu Musa Jegus a yayin wasan kwallon kafa na matasa karo na farko da aka shiryawa matasan shiyar da akaiwa taken Kano 2020 Sadiq Fakai cewa yayi shirya gasar wani dan ba ne na sanya tubalin bunkasa wasan kwallon kafa tsakanin matasan yankin daya kunshi jihohi 7,
Da yake karin haske kan yadda wasan ke kasancewa Shugaban Matasan APC cewa yayi akwai abin mamaki da alfahari yadda matasan yan wasa ke taka leda da yadda matasan suka karbi gasar da aka dan hada kan matasan,
Kan irin kalubalen da matasan arewacin kasar ke fuskanta na rashin samun dama a kungiyoyin kwallon kafa na kasa da suka hadar da kungiyar yan kasa da shekaru 15 da 17 da 20 Sadiq Fakai cewa yayi hakanne ya sanya shi gayyatar fitattun tsoffin yan wasan kasa irinsu Tijjani Babsngida da wasunsu dan ganewa idonsu irin dinbin matasan masu basira dake wannan shiya,wanda hakan zai bada damar zabar yan wasa da za a kaisu kungiyar kwallon kafa ta kasa,
Wasan da jihohi 7 ke fafatawa da kungiyoyi takwas dake gudana a jihar kano zai zama mabudi ga kungiyar data shirya dan cigaba dashi a duk shekara inji Abubakar Sadiq Saad Fakai