Kan Pillars Ta Gabatar Da Sabbin Yan Wasa Da Mai Horarwa,A wani Kwarya Kwaryan biki da aka gudanar a Hotal din Tahir karkashin jagorancin babban sakataren maaikatar matasa da bunkasa wasanni na jihar kano Alhaji Ibrahim Ahmad Sagagi ne aka gabatar da sabbin yan wasa 9 da sabon mai horarwa leonon Sociooo dan kasar faransa daya taba aiki a kasar Kamaru da afrika ta kudu da wasu kasashen Afrika
Da yake jawabi amadadin kwamishinan wasanni na jihar kano babban sakatare maaikatar Matasa da wasanni Alhaji Ibrahim Ahmed Sagagi yabawa tsohon mai horarwa Ibrahim Musa yayi wanda zai zama mataimaki sakamakon wata doka data tsaidashi zama jagoran kungiyar bisa irin kokarinsa na kai kungiyar matakan alfahari da suka hadar da cin kofin Ateo da sauran nasarori daya samu wacce babban sakatare Sagagi yace bazaaiya mantawa dasu ba, kana ya ja hankalin sabon kocin dayayi duk mai yiwuwa dan samun nasarar kungiyar da yace na cikin sahun kungiyoyin da ake alfahari dasu a Najeriya da Afrika kana ya godewa gwamnan jihar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje bisa kokarinsa na tallafawa kungiyar a koda yaushe,
Shi kuwa shugaban kungiyar Surajo Yahaya Jambul bayyana irin matakan da akabi dan daukar maihorarwa yayi da cewa matakaine da suka karfafa gwiywar shugabannin kungiyar saboda chanchantarsa.
Shikuwa sabon mai horarwar Socioo cewa yayi yazo kano pillars ne da zimmar samar da nasarar da ake bukata.
Dayake taaliki Alhaji kabiru Baita mai bawa gwamna shawara kan harkokin wasanni jan hankalin masu ruwa da tsaki na kungiyar yayi dasu hada karfi da karfe dan ganin an fidda marada kunya.