Daga .Salisu Musa Jegus
Antonio Rudiger ya ce kalaman wariyu sun yi galaba kan karar da ya shigar cewar magoya bayan Tottenham sun ci zarafi ranar 22 ga watan Disamba.
A ranar sai da aka tsayar da wasan da Chelsea ke buga wa da Tottenham, bayan da dan wasan tawagar Jamus ya ce ya ji ana yin kalaman wariya.
Ranar 6 ga watan Janairu, Tottenham ta ce da ita da ‘yan Sanda sun yi dukkan bincike, amma ba su samu gaskiyar zargin da aka yi ba.
Rudiger ya ce ”Ba a hukunta su ba daga karshe, nine da laifi kenan”.
A wani jawabi da Tottenham ta fitar, bayan kalaman Rudiger ta ce ”Ta goyi da bayan matakan da Rudiger ya dauka a halin da ya tsinci kansa kuma suna karfafa gwiwar duk dan wasan da ya ci karo da irin haka nan gaba ya sanar da mahukunta”
Ta kara da cewar ”Komai a fayyace yake kan yadda ta gudanar da bincikin, da zarar ta ci karo da wata shaida ko karin bayani za ta sanar”.
