Tsohon gwamnan jihar Imo Rochas Okoracha, ya shawarci shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da ya kori dukkanin mukarrabansa.
Okoracha ya bada shawarar ce yayin ziyarar da ya kaiwa gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule a garin Lafia, inda ya ce dukkanin ministoci da sauran mataimakan da Buhari ya nada sun gaza wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu.
Tsohon gwamnan na Imo ya ce ya zama dole shugaba Buhari ya gaggauta daukar matakan ceto Najeriya daga kangin kuncin da ta fada da kuma zubewar daraja.
Okorocha ya kara da cewar gazawar da gwamnati mai ci ta yi wajen tsare rayuka da dukiyoyin al’umma ya fusata ‘yan Najeriya matuka, dan haka kamata ya yi shugaban kasar ya maye mukarrabansa na yanzu da wadanda za su sauke nauyin hakkin da za a dora musu.
Wannan dai ba shi ne karo na farko da ake kira ga shugaba Buhari da ya sallami wasu daga cikin mukarranbansa ba, musamman ma shugabannin rundunonin tsaron kasar, sakamakon matsalolin rashin tsaro na hare-haren ‘yan bindiga da satar mutane, da kuma barazanar mayakan Boko Haram da aka shafe shekaru 10 ana jami’an tsaron Najeriya na fafatawa da su.