Dan Najeriya kuma dan asalin jihar kano dake jagorantar yan kasar Bahrain a wasan guje guje da tsalle tsalle a matakai daban daban a dunuya Abbas Abubakar Abbas a.k.a Abba Naye yace hukuri, juriya da sadaukar da kaine ya sanyashi gogayya da shahararrun yan tsere a Duniya,
A tattaunawar sa da wakilin mu Abba Naye yace wasan gudu wani wasane da ya tsinci kan sa ciki ba zato ba tsammani dan bashine wasan da yake son ba, amma dayake komai Allah ke tsara shi sai gashi ya zame masa mahuta shida sauran mutanen dake kusa dashi harma da wadanda ke iya cin gajiyar albarkar wasan,
Da yake tsokaci kan yadda matasa ya kamata su kasance dan samun nasara, cigaba da kuma samun arziki a fagen wasanni Abba Naye cewa yayi ya zama wajibi ga me neman nasara da daukaka a wasan ya zama mai sadaukar da kai da biyayya ga wasan da jagororin sa,
Kan yadda yan wasa kan chanja halaye a lokacin fa suka fara samun arziki cewa yayi kai kai kai kokadan yadda wasu yan wasa keyi shike jaza musu rashin dorewar arziki da yin dana sani daga baya,
Da yake karin bayani kan yadda aniyarsa take ga yan wasa masu tasowa cewa yayi ko yanzu na samu nasarar fidda yan wasa da dama daga Nijeriya zuwa Bahrain avwasanni tsere da kwallon kafa kuma wannan farawa nayi, dan ko yanzu inna ta shirye shiryen kai wasu a cikin wannan shekarar dan basu dama, ” akwai damanmaki da yawa da muke dashi na taimakawa amma wasu yan wasan basa shiryawa kalubale”
Ya kara da cewa ko yanzu ina da masu duba min yan wasa a gurare daban daban a Najeriya kuma lokaci zuwa lokaci suna sanar dani irin yadda yan wasan suke kuma ina gamsuwa da yadda nake samun bayanan, illa dai sai su yan wasan sun yadda da kansu kafin mu da zamu kai su mu samu karfin gwiywa,
Da yake amsa tambaya kan burin da yake dashi Abba Naye cewa yayi “ai bai wuce in taimaki mutane ba, kullum burina inga mara karfi ya zama mai karfi, in taimaki wanda ke neman taimako shine burina”