Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

A yau alhamis Gwamnan jihar kano Dr Abdullah Umar Ganduje ya bada sanarwar cire dokar kulle a fadin jihar,

A wani taron manema labarai kan cutar covid 19 da aka gugdanar a fadar gwamnatin jihar Gwamna Gabduje yace laakari da yadda ake samun saukin cutar a jihar da adduoi da alummar jihar keyi abin ayaba ne,

Daga nan sai gwamnan yace ya zama lallai akiyaye da dokokin da masana suka sanya na saka safar baki, daukar mutum 2 a baburan adaidaita sahu, da hana goyon biyu a babur mai kafa biyu abin da yace jamian tsaro zasu sanya ido dan ganin sun tabbata,

Gwamna Ganduje yace maaikatan gwamnati daga mataki na 12 zasu koma bakin aiki daga karfe 9 na safe zuwa 2 na rana haka kuma yan aji 6 na firamare dana aji 3 da 6 na sakandare zasu koma makaranta, inda za a jira Gwanatin tarayya da jin lokacin da za a bude makarantun baki daya.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *