Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

 

Kungiyar damben jihar kano ta lashe wannan gasa ne da maki goma shadaya a wasan dasuka buga da mai masaukin baki jihar Naija a filin wasan damben gargajiya dake UK Bello agarin minna

Tunda farko dai jihar katsina ne suka doke jihar nassarawa da maki Tara da uku
Yayinda jihar kano suka lallasa masu masaukin baki da maki goma babu ko daya.

Tunda farkon wasan dai dan wasan jihar kano Abdul razak Ebola shine yafara kawowa jihar kano maki Uku tahanyar buge Bahagon Audu argungu na jihar Niger

Sai dambe na biyu tsakanin dogon Aleka na jihar kano dashi da shagon Ali kanin Bello inda suka fafata suka jigata amma daga karshe dogon Aleka yasamu maki guda biyu tahanyar fiddashi daga layi har sau biyu

Dambe na uku wasane tsakanin Ali kanin Bello daga jihar kano da shagon danladi nageza inda Ali kanin Bello shima yasamu maki biyu sakamakon fita alayi da abokin damben shi sau hudu

Shikuwa shagon Asharuwa na jihar Niger yayi surrender yabada maki uku ga abokin damben shi Autan dan bunza na jihar kano
Jihar kano ta lashe wannan gasane da maki goma
Sai jihar katsina ta biyu da maki Tara
Jihar Nassarawa ta uku da maki uku

Mai masaukin jihar Niger itace tayi ta karshe basuda maki ko daya.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *