Gwamnan Jihar Jigawa Mohammed Badaru Abubakar ya sanar da buɗe iyakokin jihar da sauran jihohi, waɗanda aka rufe tun 24 ga watan Maris saboda annobar cutar korona, a cewar rahoton NAN.
Gwamnan wanda ya bayyana haka a taron manema labarai ranar Asabar a Dutse babban birnin jihar, ya ce za a buɗe zirga-zirga tsakanin jihar da sauran jihohi cikin tsauraran matakan kariya daga cutar.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya rawaito cewa buɗewar tana zuwa ne mako guda bayan an buɗe kasuwannin jihar da ke ci sati-sati.
Tuni aka sallami mutum 307 daga cikin 317 da suka kamu da cutar bayan sun warke, yayin da tara suka mutu.
“Muna ta addu’ar kada mu koma cikin irin wancan lokacin da ba shi da tabbas,” in ji gwamnan.
“Yanzu haka mutum ɗaya ne yake jinya [ta cutar korona], inda sauran da ke cibiyar killace masu korona suka warke kuma aka sallame su.
“Muna kuma gode wa Allah, a cikin kwana huɗu da suka gabata ba a samu wani da ya kamu da cutar ba. Da addu’a da kuma taimakon ‘yan Jigawa, za mu kawo ƙarshenta,” in ji Badaru.
NAN ya ce gwamnan ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta bai wa jihar tallafin naira biliyan ɗaya, ƙari a kan mota 150 cike da hatsi domin raba wa marasa ƙarfi.
Sai dai gwamnan ya ce makarantu za su ci gaba da kasancewa a rufe har zuwa lokacin da al’amura suka lafa a ƙasa baki ɗay