Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

By Abdullahi Isah

Wasu jiga jigan jam’iyar adawa ta PDP a jihar Ondo sun sanar da canja sheka zuwa jam’iyar APC mai mulki.

Daga cikin manyan ‘yan siyasar da suka bar PDP zuwa APC akwai tsohon mataimakin Gwamnan Jihar ta Ondo, Lasisi Oluboyo, da tsohon shugaban jam’iyar na farko a jihar, Samuel Awodeyi.

Kamar yadda suka bayyana a yayin bikin komawarsu APC, akwai magoya bayansu kimanin 10, 000 da suka bisu zuwa APCn.

Wannan dai na zuwa ne gabanin zaben Gwamnan Jihar ta Ondo da za’a gudanar cikin shekarar 2020 da muke ciki.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *