Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Wani yaro wanda ya nemi da mu boye sunansa dan kimanin shekara 13 yace ya zabi sanaar gwangwan ta jan Msyen Karfe a matsayin abin dogara da samun abin kalaci,

A zantawarsa sa da wakilinmu a lokacin dayayi kacibus dashi akan hanya janye da wani dunkulen karfe da wata igiya yana ja yaron yace yakan fito da sassafe kullum da bin kwararo kwararo yana Jan karfen wanda yace mayen karfe ne da yake kama masa Karafan da suke cikin kasa ko yayi.

Da yake amsa tambaya kome yasashi yin wannan Sana’a duk da cewa yarone shi a maimakon rugumar karatu sai yace “Ai Ina karatu na zamani dana addini wannan bata hanani yin komai, zaman lokacin tafiya karatun ne nake amfani dashi nayi wannan sanaar”

Kan abinda yake samu a kowace rana yaron cewa yayi yana samun Naira 500 zuwa 1000 a kullum. abin dayace yana biya Masa bukatunsa harma ya taimakawa Iyayensa,

Sau tari gwamnatoci na kukan cewa alumma basa son tashi dan yin aikin daya kamacesu amma ga ire iren wannan yaron kome hukumomin zasu ce ?

Eu kuwa bangaren yara DA matasa dakan raina Sana’a koyaya suke kallon karamin yaron dake iya hada Naira 30,000 a wata kudin da ke zaman mafin kankanta albashi ga maaikacin gwamnati a wata ?

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *