Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

A wata takarda mai dauke da sa hannun shugaban jam’iyyar na kasa, Alhaji Falalu Bello, OFR wacce aka aikewa manema labarai, daga jami’in yada labarai na jam’iyyar na kasa, Alhaji Abdul-Kadir Abubakar Kurawa.

Jam’iyyar ta PRP ta bayyana shekarar 2020 a matsayin wacce tafi kalubale a tarihin duniya saboda yadda ta ke tattare da batutuwan da suka shafi harkar lafiya da karyewar tattalin arziki.

“Shekarar 2020 na daya daga cikin shekaru mafiya wuya, ba iya Najeriya kadai ba har duniya gabadaya. Annobar Korona da alakarta da tattalin arziki da kalubalen fannin lafiya ta zama abin damuwa ga kowa”, inji sanarwar.

Jam’iyyar ta kuma jajanta yadda yan Najeriya ke shan wuya tsawon shekaru na mulkin shugaban kasa Buhari, “baza mu mantawa da da irin wahalhalu da matsi da gwamnatin Buhari da APC su ka samu a ciki ba tun daga shekarar 2015″, inji ta.

Malam Falalu ya bukaci shugaba Buhari da APC su mayar da hankali wajen warware matsalolin da al’umma ke ciki.

Jam’iyyar PRP ta ce, Yan Najeriya za su dora alhakin abinda ke damun yan kasa kan gwamnatin ”Mista Integrity”.

Sannan ta yi kira ga yan Najeriya da su hada kai da goyan bayan manufofinta don ganin an samar da ci gaban Najeriya anan Gaba.

Jam’iyyar ta kuma taya yan Najeriya Murnar bikin Sabuwar Shekara.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *