Jam’iyyar PDP ta rubuta takarda zuwa ga Shugaban ‘yan sandan Najeriya, IGP Mohammed Adamu, ta na neman a kama shugaban APC na jihar Kano.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa jam’iyyar PDP mai adawa ta nemi a cafke Alhaji Abdullahi Abbas ne saboda zarginsa da ake yi da furta kalaman kiyayya.
Alhaji Abdullahi Abbas ya yi wani jawabi, inda aka ji ya na kiran a lallasa wanda aka kama ya je zai saci akwatin zabe a 2023, wannan ya sa PDP ta kai kara.
“Ku kai hari ku hukunta duk wanda ku ka samu zai saci kuri’a a lokacin zaben 2023. Ku dauki doka da mataki mai tsauri a hannunku, babu abin da zai faru.”
KU KARANTA: Ministan Buhari ya koka da rajistar APC da ake yi
Ya cigaba da cewa: “Na ba ku umarni ku hukunta duk wanda aka samu gaban akwatin zabe ya na shirin murdiya, wannan ukuba ta ce, babu abin da zai faru.”
“Ina kira ga matasan jam’iyyarmu, su ajiye makamansu, akwai lokacin da za su yi amfani sosai.” Inji Abbas lokacin rantsar da shugabannin kananan hukumomi.
Shugaban PDP na Kano, Alhaji Shehu Wada Sagagi, ya ce sun rubuta takarda, sun aika wa shugaban ‘yan sanda na kasa da wasu hukumomin gwamnati a Najeriya.
“Ba mu yi mamaki ba, domin ya zama a jininsa, ya yi irin wannan magana. Wannan kalaman kiyayya ne.” PDP ta ce ta kai kara saboda zaman lafiyar al’umma.
Wada Sagagi ya ce duk da abin da shugaban na APC yake fada, ba zai hana a zabi jam’iyyar PDP a 2023 ba.