Tun bayan da Gwamnatin jihar kano ta mayar da asibitin Marigayi Abdullahi Wase dake yakin karamar hukumar Nasarawa zuwa asibitin koyarwa karkashin kulawar Jamiar Maitama Sule ayyuka suka kankama dan ganin ancimma burin samar da karin asibitin koyarwar mallakin jihar kano,
A wata ziyara da sabon shugaban jamiar farfesa Muktar Atiku Kurawa yakai asibitin ranar alhamis dan duba aikin yabayyanawa manema labarai cewa a gine ginen na tafiiya kamar yadda aka tsara kuma dukkanin kayayyakin da ake bukatar sawa bayan kammala ginin sun kammala sai jiran kafasu bayan gine ginen sun kammala,
Atiku Kurawa wanda ya bayyana jin dadin sa na aniyar gwamnati na samar da wannan asibiti yace tun shekara ta 2020 gwamnatin kano ta amince a Maida asibitin zuwa asbitin koyarwa mallakin jiha kuma gashi aikin na daf da kammala inda ya kara da cewa samar da asibitin zai bawa daliban jamioin mallakin jihar kano damar samun kwarewa a fanin. Kula da lafiya, tare da Samar da saukin kula da lafiya ga alummar jihar kano,