Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Alhaji Tanko Yakasai, jigo a kungiyar dattawan Arewa kuma uba ga mai taimaka wa Ganduje kan harkokin yada labarai, Salihu Tanko Yakasai ya tabbatar da cewa dansa (Salihu) yana tsare a hannun jami’an tsaro.

Kodayake, bai bayyana takamaiman hukumar tsaron da ta tsare dan nasa ba.

Yakasai a wata hira ta wayar tarho da jaridar Vanguard a safiyar ranar Asabar, 27 ga watan Fabrairu, ya ce an tsare dan nasa ne tun daga ranar Juma’a lokacin da ya tafi gidan aski kuma yana kan hanyarsa ta komawa gida.

A cewarsa, “Yana hannun jami’an tsaro ba masu satar mutane ba. Ban san wanne daga cikin hukumar tsaron ba a yanzu saboda suna da suna da yawa.

“An dauke shi ne a jiya (Juma’a) lokacin da ya je aski lokacin da yake dawowa. Amma babu wani abin damuwa tunda yana tare da jami’an tsaro ba masu satar mutane ba,” in ji Yakasai.

Idan za ku tuna, a ranar Juma’a, 26 ga watan Fabrairu ne hadimin Gwamna Ganduje na jihar Kano, Salihu Yakasai, ya bukaci gwamnatin APC ta shawo kan ta’addanci ko kuma tayi murabus.

A wallafar da Yakasai wanda aka fi sani da Dawisu yayi a shafinsa na Twitter bayan samun labarin satar ‘yan matan daga makarantar Jangebe, ya bukaci gwamnatin APC da ta kawo karshen ‘yan ta’adda ko tayi murabus.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *