Daga-Nazeefi Bala Dukawa

Jami’an lafiya dake aikin Asibitin Sheik Jeddah a Jihar Kano, sun kama katandin laimuka guda 700 aka shigo dasu daga Jihar Legas.
Tawagar Jami’an Lfiyar karkashin jagorancin Mataimakin Darkta Aminu Burji, sukai nasarar kama kayan a lokacin da ake kokarin shiga dasu cikin kasuwar kwanar Singa.
Wakilin Expressradio lokacin da yake zantawa da mutumin da ake zargi da shigo da kayan yace ” sayowa yayi daga jihar Legas kuma kudin kayan ya kai naira miliyan 2.5″.
Ya kuma roki jami’an lafiyar dasuyi masa sassauci.
Yayin da wakilinmu ya tuntubi Ma’aikatar lafiya ta Jihar Kano, tabakin Dr. shehu Usman Abdullahi, yace “akwai illar dake tattare da lemon kuma a yanzu ana fama da cututtuka iri iri dan haka zasu cigaba da sanya idanu akan abin da jama’a zasu kai bakinsu.