
Wani Fasinja ya rasa ransa akan hanyar Abuja zuwa Kano,sai dai sa’ilin da wannan gawa ta shigo jihar Kano ba’a tsaya ko Ina da ita ba sai shalkwatar Hukumar Hisbah, ta Kano, lamarin daya Sanya tsoro da firgici a zukantan Jami’an Hisbah wadan da aka rasa Wanda zai je ga wannan Gawa.
Sai dai wani abin mamaki shine an nemi lambobin wayar manyan jami’an kwamitin dake yaki da cutar covid-19 tun karfe 11 na safe har zuwa wannan lokaci hada wannan rahoto amma babu wanda ya amsa kiran wayar.
Ganin hakan yasa Hukumar Hisbah ta nemi kai wannan Gawa mutuware domin killaceta a Asibitin Kwararru na Abdullahi Wase( Nasarawa).
Mutum dai Ya rasune a cikin Mota lokacin da yake hanyarsa ta zuwa Kano daga Birnin Abuja, Kuma Dan Asalin Jamhuriyar Nijarne,
A hannu guda Shirin Duniya Tumbin giwa ya bankado cewar wannan cuta ta coronavirus ba’a shirya mata ba Duba da yadda jami’an basa daga waya.
Malam Muhammad Albukari Mika’il, Mataimakin Babban Kwamandan Hisbah bangaren ayyuka na musamman, yace “suna kokarin tuntubar wadan da al’amarim ya shafa”, sai daga karshe sun dauki wannan gawa da rakiyar jami’an tsaro sun kaita Asibitin Nasarawa kuma an karbi gawar domin gudanar da gwaji, nan kuma da kwanaki biyu za’a karbi sakamakon gwajin.