Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

,

A yayin da gwamnatin tarayyar najeriya ke kokarin sassauta dokar kulle dan saukakawa alumma bunkasa tattalin arzikin su daya girgiza sakamakon cutar covid 19,

Rahotannin alkaluman da rasuwa da yawan samun masu dauke da cutar da ake samu kullum da hukumar dakile cutuka masu yaduwa ke fitarwa a kullum na nuni dacewa najeriya na fuskantar hadarin komawa gidan jiya,

Tun bayan da shugaba Mohammadu Buhari ya amince da zagaye na biyu na sassauta dokar kulle cutar ke karuwa, a karshen watan nanne hukumar dakile cututtuka ta NASA NCDC ta fitar da sabbin alkaluman cutar 561 da aka tabbatar sun kamu da mutane 17 da suka rasu a Najeriya,

Duk da cewa babu sabuwa jiha da cutar ta bulla a awa 24, kawo iyanzu najeriya nada adadin mutane 25694 da suka kamu da cutar inda aka sallami 9746 yayin da 590 suka rasu a Jahohi 35 hadda Abuja,

Sabbin Alkaluman sun nuna Lagos na kan gaba (200), Edo(119), Kaduna(52), FCT(52), Niger(32), Ogun(19), Ondo(16), Imo(14), Plateau(11), Abia(8), Oyo(8), Bayelsa(7), Katsina(6),Kano(5), Bauchi(3), Osun(3), Kebbi(3), Borno(2), Jigawa(1).

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *