Bola Tinubu, tsohon gwamnan jihar Legas kuma jagoran jam’iyyar APC, ya dawo gida Nigeria bayan shafe wata guda a waje
Wasu rahotanni a farkon watan Janairu sun fara yada rahoton cewa an kwantar da Tinubu a wani asibitin kasar Faransa
Daga baya, wata sanarwa daga Ofishin yada labaran Tinubu ta karyata rahotanni tare da bayyana cewa yana cikin koshin lafiya
Jagoran jam’iyyar APC kuma tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Tinubu, ya dawo gida Nigeria bayan batan dabon wata guda.
An ga Tinubu a filin jirgin sama na Murtala Muhammed (MMIA) da ke Legas bayan saukarsa da yammacin ranar Lahadi, kamar yadda TheCable ta rawaito.
A farkon watan Janairu ne rahotanni suka fara cewa an kwantar da Tinubu a wani asibiti a kasar Faransa bayan ya kamu da rashin lafiya.
Wasu daga cikin rahotannin sun bayyana cewa Tinubu ya kamu da cutar korona, amma daga baya sanarwa daga ofishinsa ta karyata rahotannin.
Sanarwar ta bayyana cewa Tinubu ya karbi sakamakonsa na gwaji tun a gida Nigeria kuma an sake gwada shi a waje amma duk ba’a same shi da kwayar cutar korona ba.