Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Ina son zama babban Alkalin wasan kwallon kafa a Duniy,

Sabanin yadda matasa ke zake zabin zama yan wasan a cikin jerin wasanni a duniya wani yaro mai shekaru 12 Bello Musa ya zabii zama alkalin wasan kwallon kafa duk da irin kalubalen da alkalancin wasan ke dashi,

A tattaunawarsa da expressradiofm.com Bello Musa yace ya zabi zama alkalin wasa ne saboda yadda ya tashi da sha’awar zama alkalin inda yace” Tun ina dan shekara 10 nake da shaa’war nayi alkalanci a wasan kwallon kafa kuma gashi burina ya fara cika har gashi ina shiga cikin manyan wasa a jihar kano wanda kuma hakan wani matakine dana fara takawa,

Dayake karin haske kan yadda wakilinmu.ya tarar dashi yana alkalancin wani wasa Bello Musa cewa yayi wannan shine wasansa na 3 a ranar inda yayi alkalanci a wasan safe da wasan rukuni na 2 na rana da kuma wasan sada zmunta na yamma,

Da yake amsa tambaya kan irin kalubalen da yake fuskanta kasancewarsa yaro mai karancin shekaru Bello cewa yayi babu wani kalubale tunda ina da ilimin yadda zan jagoranci wasa duk girmansa inda yace ” ai alkali ne keda wasan a hannunsa ba wasanne keda alkalin ba” dan haka ni bawani kalubale illa na gane yadda wasan da yan wasan suke

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *