Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Rade radin da ake a kafar sada zumunta da wasu kafafen radio na cewa dan takarar gwamnan jihar kano na jamiyyar PDP a shekara ta 2019 Abba Kabir Yusif zai balle daga jamiyyar kanzon kurege ce.

A wata takarda da kakakin dantakarar Ibrahim Adam ya aikawa solacebase tace ba gaskiya bane irin abubuwan da ake fada a kafafen sada zumunta na cewa Abba Kabir zai balle saboda ana zato jagoran kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso zai sauya Dan Takara a zaben 2023 inda ake cewa zai maida ita zuwa ga Abba Bichi,

Inda yace kawo iyanzu ba takarace gaban Abba yusif ba abin da a kasa a gaba shine yadda zaa cigaba da bunkasa akidar kwankwasiyya ta cigaban alumma ba takara ba, inda ya kara da cewa mulki na Allah ne kuma shiyake bayarwa ga wanda ya so a lokacin daya so.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *