Daga-Adamu Aminu Fagge
Ma’aikatar kananan hukumomi ta jahar Kano da hadin gwaiwa da hukumar yaki da cin hanci ta jahar Kano ICPC,ta gudanar da taron bita ga zababbun shugabannin kananan hukumomi da sakatarorinsu domin kaucewa fadawa hannun hukumar
Da yake bayani shugaban hukumar ICPC na jihar Kano, Mallam Almu Dan-Musa ya bayyana cewar hukumarsa ta shirya bitar ne ta yadda shuwagabanin kananan hukumomin zasu kashe kudin akan ka’ida ta yadda zasu kaucewa shiga wasu laifuffuka da suka sabawa dokokin hukumar.
Babban sakataren kananan hukumomin na jahar Kano Sale Ado Minjibir wanda ya wakilci Kwamishinan kananan hukumomin na jihar Kano, Murtala Sule Garo, yace wañnan taróne da aka shirya domin karawa juna sani ta yadda zai zamo akwai kyakkyawar alaka tsakanin shuwagabanin kananan hukumomin da hukumar hana cin hanci da rashawa ta ICPC ta yadda za’a akaucewa samun su da cin hanci da rashawa
Taron ya sami halartar shuwagabanin kananann hukumomin na jahar Kano tare da sakatarorinsu.