Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.
Shugaban Hukumar KAROTA Dr. Babbaf Babba Dan’agundi

Hukumar dake kula da zirga zirga da kawar da cin koson ababan hawa ta Jihar Kano, KAROTA, ta kama kama kwayoyi da kudin su ya haura naira miliyan 25 a unguwar Sabon Gari.

Kwagoyin dai na Kara kuzarin mazane Arofranil, Kuma lambar sahalewar Hukumar NAFDAC a jiki, sun kama kayan sakamakon rahoton sirri da suka samu.

Kayan da ake zargin na jabune an kamusne a tashar Motar New road a Sabon Gari, a cikin wata babbar motar za’a fara rabasu.

kwagoyin dai adadinsu yakai Sachets dubu biyar Kuma suna hannun Hukumar KAROTA, sai dai Mai kayan ya cika wandonsa da iska.
Hukumar KAROTA tace zata mika kwagoyin ga kwamitin dake yaki da jabun kwayoyi na Jihar Kano domin daukar mataki na gaba.

A cikin sanarwar da Jami’in Hulda da jama’a na Hukumar Nabilisi Abubakar Kofar Na’isa ya fitar, tace Manajan Daraktan Hukumar KAROTA Dr. Baffa Babba Dan’agundi, ya bukaci alumma da su cigaba da baiwa Hukumar goyon baya domin ta Kai Jihar nan ga wani Babban mataki.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *