
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, ta jaddada aniyarta ta yin aiki tare da al’umma da gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu domin tallafawa marassa galihu dake Jihar Kano.
Babban Kwamandan Hukuamr Hisbah na Jihar Kano, Dr. Harun Muhammad Sani Ibn Sina, yayi kiran a lokacin da Babban Darakta n cibiyar kyautata rayuwar marassa galihu ta GIOPINI, ya kawo masa ziyarar aikishalkatar Hukumar Hisbah ta Jihar Kano dake Sharada.
Ibn Sina, yace Hukumar Hisbah ta kokarin kawar da dukkan ayyukan badala da tare da umartar jama’a zuwa kyakykyawa.
Da yake nasa jawabin Alhaji, Shugaban Kungiyar kyautata rayuwar marassa galihu, ya yabawa Hukumar Hisbah, bisa rahoton da suka samu na kyautatawa Marassa karfi da mabukata dake wannan jiha , ya Kuma bayar da tabbaci cewa Kungiyar zatai aiki tare da shalkwatar Hukumar Hisbah ta Jihar Kano domin kaiwa ga aci.
Lawan Ibrahim Fagge
Public Relations Officer.