
Babban Kwamandan HISBAH na jihar Kano Dr. Ustaz Harun Muhammad Sani ibn Sina, yace “dakarun Hisbah sun kama Motoci guda biyar makare da Giya a cikin su.
Wadan nan motoci sun kutso jihar Kano duk da cewa an rufe iyakokin jihar nan, haka suka yi dabara tare da satar hanya suka dakko dakon barasar batare da la’akari da halin da ake ciki na annobar cutar covid-19 ba.
Babban Kwamandan Hisbar, yayi kira ga Al’umma “da a kara komawa ga Allah, kowa ya tuba daga irin laifukan da yake tafkawa domin samun sauki daga cutar covid-19.
Babban Kwamanda Dr. Harun Muhammad Sani ibn Sina, yayi addu’a ga dukkan jami’an da suka taimaka wajen Wannan aiki, Allah yayi mana jagora ya bamu da cewa, ya kuma bamu lafiya da zama lafiya, Ya yaye mana wannan Annoba da ake fama da ita,Amin