Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.
Dakarun Hisbah na Jihar Kano

Sakamakon koken da wasu daga cikin Jami”an Hisbah na Jihar Kano sukai na cewar ba’a biyasu alawus alawus din su ba,

Yanzu haka dai Babban Kwamadan Hisbah na Jihar Kano Dr. Harun Muhammad Sani Ibn Sina, yace iya abin daya sani shine duk kan jami’in daya tsaya a bakin aiki za’a biyashi hakkinsa.

Yana mai cewa bai karbi korafin kowa ba kan cewar ba’a biyashi hakkinsa ba, yace duk jami’in da ba a biyashi ba, yakai masa korafi domin daukar mataki.

Lokacin da yake zantawa da tashar redio Express a yammacin ranar Alhamis yace bai san cewa wasu Dakarun Hisbah sunyi zanga zanga ko koke ba.

Ya bayar da tabbacin cewa hukumar Hisbah zata cigaba da baiwa walwalar jam’inta kulawar data dace.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *