Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Babbab kwamandan hukumar hisbah na jihar kano Dr. Harun Muhammad Sani Ibn sina ya firta hakan a lokacin taron manema labarai daya kirawo a shelkwatar Hisbah dake Sharada a jihar Kano.

Ibn Sina yace tun da farko yaron tsintarsa akai kuma yakai wajen watanni 8 wajen jami’an Hisbah na Fagge, inda daga bisani wata mata da mai suna Jamila ta nemi a bata yaron domin tacigaba da rainonsa.

Sai dai kafin kwamadan ya bayar da yaron ga wannan mata sai daya kirawo mai unguwar Sabon Gari, wanda akai yarjejeniyar cewa duk wata matar zata rika kawo yaron ana ganinsa.

Daga bisani sai aka samu labarin wannan mata takai yaron zuwa jihar Imo lamarin dayasa aka fara zargin ko an sayar da yaronne.

Kwamadan Hisbar na jihar Kano, yace zuwa yanzu an kawo yaron yana kuma cikin koshin lafiya, ita kuma matar da mai unguwar sabon Gari suna hanun hukumar dake yaki da safarar bil adama ta NAFTB reshen jihar Kano domin acigaba da bincike.

Ibn Sina yace babban kuskuren da Kwamadan Hisbah na Fagge yayi shine bayar da yaron batare da sanin Shelkwataba ko kuma wasu jami’ai na karamar hukumar Fagge, yana mai cewa shima Kwamandan Faggen za’a ladaftar dashi bisa tanadin dokokin hukumar Hisbah.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *