Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wata matar aure wadda take hada hadar tabar wiwi.
Babban Kwamandan Hisbah na Jihar Kano Dr. Harun Muhammad Sani Ibn Sina ya firta hakan a lokacin da yake zantawa da Express radio.
Ibn Sina, yace “abin ta kaicine ace shaye shaye ya tsallake kan maza harda matan aure, ya cigaba da cewar “matar dan tane ya tseguntawa jami’an Hisbah irin laifin da take aikawa.
Babban Kwamandan Hisbar, ya ce “sun kama tirela 5 wadanda suke dauke da giya a ciki, yana macewa da zarar kotu ta shalewa Hukumar zaitai bikin farfasasu”.
Ibn Sina, ya kuma yi kira ga magidanta dasu rika sanya idanu akan kai komin matansu dan gudun kitso da kwarkwata.